24 Mayu 2021 - 19:11
Faransa Ta Yi Gargadi Game Da Nuna Wariya A Isra’ila

Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya yi gargardi game da yiyuwar barkewar rikicin nuna wariya a Isra’ila, idan ba’a samar da kasashe biyu ba Isra’ila da Falasdinu.

ABNA24 : Game da abunda ya faru kwanakin baya inda aka samu rikici tsakanin yahudawa ‘yan Isra’ila da Larabawa Falasdinawa, yana da kyau a gaggauta samar da kasashe biyu domin kawo karshen yiyuwar barkewar rikici mai nasaba da nuna wariya da banbanci a cewar ministan harkokin wajen kasar ta Faransa a muhawarar Grand Jury ta gidan talabijin na RTL/Le Figaro/LCI .

Kan hakan ne a cewarsa ya kamata a gaggauta samar da mafita ta siyasa a Jean-Yves Le Drian.

A halin da ake ciki dai sojojin Isra’ila da kungiyar Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, tun ranar Juma’a bayan shafe kwanaki na rikici, wanda ya yi sanadin rasa rayukan Falasdinawa 248, da kuma ‘yan Isra’ila 12.

342/